Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 25:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.

2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.

3. Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.

4. Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.

5. Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.

6. Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’

7. Duk 'yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.

8. Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’

9. Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

10. Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa.

11. Daga baya sai waɗancan 'yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’

Karanta cikakken babi Mat 25