Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 24:36-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. “Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

37. Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.

38. Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi,

39. ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.

40. A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

41. Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

42. To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.

43. Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.

44. Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”

45. “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?

46. Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.

Karanta cikakken babi Mat 24