Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 24:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.

11. Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.

12. Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.

13. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.

14. Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”

15. “Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),

16. to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.

17. Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.

18. Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.

Karanta cikakken babi Mat 24