Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.

5. Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.

6. Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u,

7. a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.

8. Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.

Karanta cikakken babi Mat 23