Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Yesu ya yi wa jama'a da almajiransa magana, ya ce,

2. “Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.

3. Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.

4. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.

5. Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.

6. Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u,

7. a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.

Karanta cikakken babi Mat 23