Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 19:19-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”

20. Saurayin ya ce masa, “Ai, duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?”

21. Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

22. Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

23. Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama.

24. Har wa yau ina gaya muku, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

25. Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

26. Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”

27. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi mun bar kome, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?”

28. Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.

29. Kowa ya bar gidaje, ko 'yan'uwa mata, ko 'yan'uwa maza, ko uwa, ko uba, ko 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.

30. Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”

Karanta cikakken babi Mat 19