Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 19:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya bar ƙasar Galili, ya shiga ta Yahudiya, wadda take ƙetaren Kogin Urdun.

2. Taro mai yawan gaske suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.

3. Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa a kan kowane dalili?”

4. Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karantawa ba, cewa, wanda ya halicce su tun farko, dā ma ya yi su, namiji da tamata?”

5. Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutum ya bar uwa tasa da ubansa, ya manne wa mata tasa. Haka su biyun nan su zama jiki guda.

6. Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”

7. Sai suka ce masa, “To, don me Musa ya yi umarni a ba da takardar kisan aure, a kuma saki matar?”

8. Ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya yardar muku ku saki matanku, amma ba haka yake ba tun farko.

9. Ina kuma gaya muku, kowa ya saki mata tasa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

10. Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutum da mata tasa yake, ashe ma, rashin yin aure ya fi amfani.”

11. Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa.

12. Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”

13. Sa'an nan aka kawo masa yara ƙanana domin ya ɗora musu hannu, ya yi musu addu'a, amma almajiran suka kwaɓe su.

Karanta cikakken babi Mat 19