Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 18:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?”

2. Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu,

3. ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.

4. Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.

5. “Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.

6. Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”

7. “Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!

Karanta cikakken babi Mat 18