Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 16:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.

2. Ya amsa musu ya ce, “In magariba ta yi, kuka ga sama ta yi ja, kukan ce, ‘Aha, gari zai yi sarari.’

3. Da safe kuma in kun ga sama ta yi ja, ta kuma gama gari, kukan ce, ‘Yau kam, za a yi hadiri.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan.

4. 'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.

5. Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba.

6. Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”

7. Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo gurasa ba fa!”

8. Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?

9. Ashe, har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka ɗauka?

10. Ko kuma gurasan nan bakwai na mutum dubu huɗu, manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

11. Yaya kuka kasa ganewa? Ba zancen gurasa na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”

12. Sa'an nan ne fa suka fahimta cewa, ba ce musu ya yi, su yi hankali da yistin gurasa ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.

Karanta cikakken babi Mat 16