Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 14:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.

2. Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”

3. Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.

4. Don dā ma Yahaya ya ce masa bai halatta ya zauna da ita ba.

5. Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne.

6. To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,

7. har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa.

Karanta cikakken babi Mat 14