Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 13:42-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.

43. Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

44. “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”

45. “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.

46. Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”

47. “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.

48. Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.

49. Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,

50. su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”

51. “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”

52. Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”

53. Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan.

54. Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan?

55. Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?

56. 'Yan'uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?”

57. Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”

58. Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.

Karanta cikakken babi Mat 13