Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 12:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?

5. Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa?

6. Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan.

7. Da kun san ma'anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba.

8. Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”

9. Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu.

10. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne.

11. Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba?

12. Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.”

13. Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan.

14. Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.

15. Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.

16. Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.

17. Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,

Karanta cikakken babi Mat 12