Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.

2. To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,

3. su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

4. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji, da abin da kuka gani.

5. Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.

6. Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”

7. Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?

8. To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.

9. To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa.

Karanta cikakken babi Mat 11