Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 10:39-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”

40. “Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.

41. Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.

42. Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”

Karanta cikakken babi Mat 10