Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 1:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.

2. Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da 'yan'uwansa,

3. Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (uwa tasu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram,

4. Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,

5. Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,

6. Yesse ya haifi sarki Dawuda.Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),

7. Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,

8. Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya,

Karanta cikakken babi Mat 1