Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:42-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. “Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku.

43. In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa. [

44. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

45. In kuwa ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke ta. Zai fiye maka ka shiga rai da gurguntaka, da a jefa ka Gidan Wuta da ƙafa biyu. [

46. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

47. In kuma idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.

48. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.

49. Da wuta za a tsarkake kowa, kamar yadda ake tsarkake abu da gishiri.

50. Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”

Karanta cikakken babi Mar 9