Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:34-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wane ne babbansu.

35. Sai ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son yă zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.”

36. Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu,

37. “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

38. Sai Yahaya ya ce masa, “Malam, mun ga wani na fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

39. Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai, ba wanda zai yi wata mu'ujiza da sunana, sa'an nan, nan da nan ya kushe mini.

40. Ai, duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.

41. Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.

42. “Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku.

43. In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa. [

44. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

45. In kuwa ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke ta. Zai fiye maka ka shiga rai da gurguntaka, da a jefa ka Gidan Wuta da ƙafa biyu. [

46. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

47. In kuma idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.

48. A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.

Karanta cikakken babi Mar 9