Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:31-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”

32. Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambaya tasa.

33. Suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawarar me kuka yi a hanya?”

34. Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wane ne babbansu.

35. Sai ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son yă zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.”

36. Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu,

37. “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

Karanta cikakken babi Mar 9