Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”

2. Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu,

3. tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya.

4. Sai Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.

5. Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”

6. Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.

7. Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”

8. Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.

9. Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

10. Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna komece ce ma'anar tashi daga matattu.

11. Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya yă fara zuwa?”

12. Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi?

13. Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”

Karanta cikakken babi Mar 9