Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 8:25-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau.

26. Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”

27. Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa nake?”

28. Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.”

29. Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.”

30. Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.

31. Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.

32. Ya ko faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa.

33. Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al'amuran Allah sai na mutane.”

34. Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

35. Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa ya yi.

Karanta cikakken babi Mar 8