Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 8:16-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Suka yi magana da juna a kan ba su da gurasa.

17. Da yake Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Don me kuke zancen ba ku da gurasa? Ashe, har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take?

18. Kuna da idanu, ba kwa gani ne? Kuna da kunnuwa, ba kwa ji ne? Ba kwa kuma tunawa ne?

19. Da na gutsuttsura wa mutum dubu biyar gurasan nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.”

20. “To, gurasa bakwai da na gutsuttsura wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.”

21. Sai ya ce musu, “To, har yanzu ba ku fahimta ba?”

22. Suka iso Betsaida. Aka kawo masa wani makaho, aka roƙe shi ya taɓa shi.

23. Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yau a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi cewa, “Kana iya ganin wani abu?”

24. Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa nake ganinsu, suna yawo.”

25. Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau.

26. Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”

27. Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa nake?”

28. Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.”

29. Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.”

30. Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.

Karanta cikakken babi Mar 8