Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 6:45-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Nan da nan ya sa almajiransa su shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Betsaida, kafin ya sallami taron.

46. Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu'a.

47. Da magariba ta yi, jirgin na tsakiyar teku, Yesu kuwa na nan kan tudu shi kaɗai,

48. da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska na gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su,

49. amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka zaci fatalwa ce, suka yi kururuwa,

50. domin duk sun gan shi, sun kuwa firgita. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, ni ne, kada ku ji tsoro.”

51. Sa'an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai,

52. don ba su fahimci al'amarin gurasan nan ba, saboda zuciyarsu ta taurare.

Karanta cikakken babi Mar 6