Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 3:26-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo.

27. Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.

28. “Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta,

29. amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.”

30. Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”

31. Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je.

32. Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.”

33. Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?”

34. Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana!

35. Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.”

Karanta cikakken babi Mar 3