Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 3:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.”

22. Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”

23. Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan?

24. Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba.

25. Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba.

26. Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo.

27. Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.

28. “Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta,

Karanta cikakken babi Mar 3