Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 3:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa.

14. Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa'azi.

15. Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu.

16. Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus,

17. da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa.

18. Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane,

19. da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.Sa'an nan ya shiga wani gida.

20. Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci.

21. Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.”

22. Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”

23. Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan?

Karanta cikakken babi Mar 3