Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 3:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu.

2. Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.

3. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.”

4. Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru.

5. Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.

6. Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.

7. Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya,

8. da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi.

9. Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda,

10. saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi.

11. Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.”

12. Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.

13. Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa.

Karanta cikakken babi Mar 3