Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 2:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. suna cewa, “Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake! Wa yake da ikon gafarta zunubi banda Allah kaɗai?”

8. Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?

9. Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya’?

10. Amma don ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–

11. “Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”

12. Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”

13. Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.

14. Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

15. Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne;

16. to, da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, suka ce wa almajiransa, “Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

17. Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”

18. To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?”

19. Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.

Karanta cikakken babi Mar 2