Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 16:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita.

6. Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi!

7. Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.”

8. Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro.[

9. Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai.

10. Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda dā suke tare da shi, ta tarar suna baƙin ciki, suna kuka.

11. Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.

12. Bayan haka ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa'ad da suke tafiya ƙauye.

13. Suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.

14. Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.

15. Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara.

16. Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.

17. Za a ga waɗannan mu'ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato da sunana za su fitar da aljannu, za su yi magana da waɗansu baƙin harsuna,

18. za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”

Karanta cikakken babi Mar 16