Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 16:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa.

2. A ranar farko ta mako, da assussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa.

3. Suna ce wa juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?”

4. Da suka ɗaga kai, suka ga, ashe, an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa, ƙato ne ƙwarai.

5. Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita.

6. Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi!

7. Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.”

Karanta cikakken babi Mar 16