Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 15:43-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

44. Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa.

45. Da ya san haka daga bakin jarumin ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin.

46. Sai Yusufu ya sayi likkafanin lilin. Da ya sauko da Yesu, ya sa shi a likkafanin lilin ɗin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, ya kuma mirgina wani dutse a bakin kabarin.

47. Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yusufu sun ga inda aka sa shi.

Karanta cikakken babi Mar 15