Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 15:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.

2. Bilatus ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗa.”

3. Sai manyan firistoci suka yi ta kai ƙararsa a kan abubuwa da yawa.

4. Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganu da suke ba da shaida a kanka!”

5. Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.

6. To, a lokacin idi kuwa Bilatus ya saba sakar musu kowane ɗan sarƙa guda da suka roƙa.

7. Akwai wani wai shi Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu 'yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen.

8. Jama'a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi.

9. Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

10. Don ya gane, saboda hassada ne manyan firistoci suka bashe shi.

11. Amma manyan firistocin suka zuga jama'a, gwamma ya sakar musu Barabbas.

12. Sai Bilatus ya sāke ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da wanda kuke kira Sarkin Yahudawa?”

13. Sai suka sāke yin ihu suka ce, “A gicciye shi!”

14. Bilatus ya ce musu, “Ta wane hali? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma su, sai ƙara ɗaga murya suke yi, suna cewa, “A gicciye shi!”

15. Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.

16. Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.

17. Suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a kā.

Karanta cikakken babi Mar 15