Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:52-72 Littafi Mai Tsarki (HAU)

52. shi kuwa ya bar musu mayafin, ya gudu huntu.

53. Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. Duk manyan firistoci da shugabanni da malaman Attaura suka taru a wurinsa.

54. Bitrus kuma ya bi shi daga nesa nesa, har cikin gidan babban firist ɗin, ya zauna cikin dogaran Haikali, yana jin wuta.

55. To, manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba.

56. Da yawa kam, sun yi masa shaidar zur, amma bakinsu bai zo ɗaya ba.

57. Daga baya kuma waɗansu suka taso, suka yi masa shaidar zur suka ce,

58. “Mun ji ya ce, wai zai rushe Haikalin nan da mutane suka gina, ya gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba.”

59. Duk da haka dai shaida tasu ba ta zo ɗaya ba.

60. Sai babban firist ya miƙe a tsakiyarsu ya tambayi Yesu ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

61. Amma yana shiru abinsa, bai amsa kome ba. Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “To, ashe, kai ɗin nan ne Almasihu Ɗan Maɗaukaki?”

62. Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.”

63. Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Wace shaida kuma za mu nema?

64. Kun dai ji saɓon da ya yi! Me kuka gani?” Duk suka yanke masa shari'a a kan ya cancanci kisa.

65. Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa.

66. Bitrus kuwa na ƙasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.

67. Da ta ga Bitrus na jin wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Banazaren nan Yesu!”

68. Amma ya musa ya ce, “Ni ban ma san abin da kike faɗa ba, balle in fahimta.” Sai ya fito zaure. Zakara kuwa ya yi cara.

69. Sai baranyar ta gan shi, ta sāke ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma nasu ne.”

70. Amma ya sāke musawa. Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don Bagalile ne kai.”

71. Sai ya fara la'antar kansa, yana ta rantserantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da kuke faɗa ba.”

72. Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.

Karanta cikakken babi Mar 14