Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:42-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni ɗin nan ya matso!”

43. Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabanni ne suka turosu.

44. To, mai bashe shi ɗin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi, ku tafi da shi a rirriƙe.”

45. Da zuwansa kuwa ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya shugaba!” sai ya yi ta sumbantarsa.

46. Su kuwa suka danƙe Yesu, suka kama shi.

47. Amma ɗaya daga cikin na tsaye, ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunne.

48. Sai Yesu ya ce musu, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi?

49. Kowace rana ina tare da ku a Haikalin ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa domin a cika Littattafai.”

50. Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

51. Sai wani saurayi, daga shi sai mayafi, ya bi shi. Suka kai masa cafka,

52. shi kuwa ya bar musu mayafin, ya gudu huntu.

53. Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. Duk manyan firistoci da shugabanni da malaman Attaura suka taru a wurinsa.

54. Bitrus kuma ya bi shi daga nesa nesa, har cikin gidan babban firist ɗin, ya zauna cikin dogaran Haikali, yana jin wuta.

55. To, manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba.

56. Da yawa kam, sun yi masa shaidar zur, amma bakinsu bai zo ɗaya ba.

Karanta cikakken babi Mar 14