Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:40-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Har wa yau kuma ya sāke dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, sun kuwa rasa abin da za su ce masa.

41. Ya sāke komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

42. Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni ɗin nan ya matso!”

43. Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabanni ne suka turosu.

44. To, mai bashe shi ɗin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi, ku tafi da shi a rirriƙe.”

45. Da zuwansa kuwa ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya shugaba!” sai ya yi ta sumbantarsa.

46. Su kuwa suka danƙe Yesu, suka kama shi.

47. Amma ɗaya daga cikin na tsaye, ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunne.

48. Sai Yesu ya ce musu, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi?

49. Kowace rana ina tare da ku a Haikalin ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa domin a cika Littattafai.”

50. Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

51. Sai wani saurayi, daga shi sai mayafi, ya bi shi. Suka kai masa cafka,

Karanta cikakken babi Mar 14