Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 14:30-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.”

31. Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Dukansu ma haka suka ce.

32. Sai suka isa wani wuri, wai shi Getsamani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna nan har in yi addu'a.”

33. Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.

34. Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.”

35. Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu'a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokaci.

36. Sa'an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”

37. Ya komo ya samu suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa'a ɗaya ba?

38. Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

39. Sai ya sāke komawa, ya yi addu'a, yana maimaita maganar dā.

40. Har wa yau kuma ya sāke dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, sun kuwa rasa abin da za su ce masa.

41. Ya sāke komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

42. Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni ɗin nan ya matso!”

Karanta cikakken babi Mar 14