Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 13:30-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.

31. Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

32. “Amma fa wannan rana ko wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da suke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

33. Ku kula, ku zauna a faɗake, kuna addu'a, domin ba ku san sa'ar da lokacin zai yi ba.

34. Kamar mutum ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta yaransa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake.

35. To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,

36. kada ya zo kwaram, ya samu kuna barci.

37. Abin kuwa da na gaya muku, ina gaya wa kowa ne, shi ne ku zauna a faɗake.”

Karanta cikakken babi Mar 13