Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 13:23-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.”

24. “Amma lokacin nan, wato bayan tsabar wahalan nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba.

25. Taurari za su riƙa faɗawa daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

26. A sa'an nan ne za a ga Ɗan Mutum na zuwa cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka.

27. Sa'an nan zai aiko mala'ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga iyakar duniya har ya zuwa iyakar sama.”

28. “Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.

29. Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan abubuwa na aukuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake,

30. Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.

Karanta cikakken babi Mar 13