Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:18-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,

19. “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.

20. To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba.

21. Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka.

22. Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu.

23. To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

24. Sai Yesu ya ce musu, “Ba saboda wannan ne ya sa kuka ɓata ba? Wato don ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.

25. Domin in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala'ikun da suke Sama ake.

26. Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’?

27. Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”

28. Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma duka?”

29. Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

30. Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’

Karanta cikakken babi Mar 12