Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 12:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama'a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.

13. Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin magana tasa.

14. Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?

15. Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku kawo mini dinari in gani.”

16. Suka kawo masa. Ya ce musu, “Suran nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.”

17. Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.

18. Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,

19. “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.

20. To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba.

21. Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka.

22. Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu.

Karanta cikakken babi Mar 12