Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 11:28-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?”

29. Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.

30. To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.”

31. Sai suka yi muhawara da juna, suka ce, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

32. Ma kuwa ce, ‘Ta mutum ce’?” Suna kuwa jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne.

33. Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”

Karanta cikakken babi Mar 11