Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 11:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la'anta ya bushe!”

22. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah.

23. Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.

24. Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.

25. Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku. [

26. Amma in ba kwa yafewa, haka Ubanku da yake Sama ma ba zai yafe muku laifofinku ba.]”

27. Suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka zo wurinsa,

28. suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?”

29. Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.

Karanta cikakken babi Mar 11