Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 10:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai Yesu ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.

17. Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”

18. Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci sai Allah kaɗai.

19. Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

20. Sai ya ce masa, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”

21. Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

22. Da jin wannan magana gabansa ya fāɗi, ya tafi yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

23. Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!”

24. Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku 'ya'yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah!

Karanta cikakken babi Mar 10