Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 10:13-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su.

14. Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

15. Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

16. Sai Yesu ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.

17. Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”

18. Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci sai Allah kaɗai.

19. Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

20. Sai ya ce masa, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”

21. Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

22. Da jin wannan magana gabansa ya fāɗi, ya tafi yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

23. Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!”

24. Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku 'ya'yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah!

25. Zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26. Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27. Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.”

Karanta cikakken babi Mar 10