Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 1:40-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.”

41. Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”

42. Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka.

43. Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan,

44. ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

45. Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al'amarin ko'ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko'ina.

Karanta cikakken babi Mar 1