Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:26-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa.

27. Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’

28. Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

29. Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.

30. Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.

31. “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su?

32. Kamar yara suke da suke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.’

33. Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da iska.’

34. Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’

35. Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne ake tabbatar da gaskiya tata.”

36. Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin.

37. Sai ga wata matar garin, mai zunubi, da ta ji Yesu na cin abinci a gidan Bafarisiyen, ta kawo wani ɗan tandu na man ƙanshi,

38. ta tsaya a bayansa a wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin.

39. To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”

40. Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.”

41. Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.

42. Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?”

43. Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.”

Karanta cikakken babi Luk 7