Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 4:32-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.

33. A majami'ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce,

34. “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

35. Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.

36. Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.”

37. Labarinsa duk ya bazu ko'ina a kewayen ƙasar.

38. Sai ya tashi daga majami'a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita.

39. Sai ya tsaya a kanta, ya tsawata wa zazzaɓin, ya kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.

40. A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.

41. Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.

42. Da gari ya waye ya fita, ya tafi wani wurin inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu ne su tsaishe shi, don kada ya tashi daga gare su,

43. amma ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa bisharar Mulkin Allah, domin saboda wannan nufi ne aka aiko ni.”

44. Sai ya yi ta yin wa'azi a majami'un ƙasar Galili.

Karanta cikakken babi Luk 4