Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 3:21-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre,

22. Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”

23. Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,

24. Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu,

25. Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya,

26. Najaya ɗan Ma'ata, Ma'ata ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yahuza,

27. Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri,

28. Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Almadama, Almadama ɗan Er,

29. Er ɗan Yosi, Yosi ɗan Eliyezer, Eliyezar ɗan Yorima, Yorima ɗan Matat, Matat ɗan Lawi,

30. Lawi ɗan Saminu, Saminu ɗan Yahuza, Yahuza ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Eliyakim,

31. Eliyakim ɗan Malaya, Malaya ɗan Mainana, Mainana ɗan Matata, Matata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda,

32. Dawuda ɗan Yesse, Yesse ɗan Obida, Obida ɗan Bo'aza, Bo'aza ɗan Salmon, Salmon ɗan Nashon,

33. Nashon ɗan Amminadab, Amminadab ɗan Aram, Aram ɗan Hesruna, Hesruna ɗan Feresa, Feresa ɗan Yahuza,

Karanta cikakken babi Luk 3