Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 23:32-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.

33. Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.

34. Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.

35. Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”

36. Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,

37. suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”

38. Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”

39. Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!”

40. Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa?

41. Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.”

42. Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.”

43. Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”

Karanta cikakken babi Luk 23