Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 21:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali.

2. Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki.

3. Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka.

4. Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

5. Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce,

6. “In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan'uwansa da ba a baje shi ba.”

7. Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”

8. Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.

9. In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

Karanta cikakken babi Luk 21