Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 2:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.

2. Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya.

3. Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi.

4. Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),

5. don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki.

6. Sa'ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi.

7. Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.

8. A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.

9. Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya,

10. Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane.

11. Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.

Karanta cikakken babi Luk 2